Home KetareAmurka ta turo Jirage marasa matuka zuwa Najeriya don tattara bayanai kan ‘Yan Ta’adda

Amurka ta turo Jirage marasa matuka zuwa Najeriya don tattara bayanai kan ‘Yan Ta’adda

33 views

Amurka ta tura jiragen sama marasa matuka (drones) zuwa Nigeria domin taimakawa wajen tattara bayanan sirri kan kungiyoyin ‘yan ta’adda a arewacin kasar.

Daraktan yada bayanai na Hedikwatar Tsaron Najeriya ya tabbatar da cewa Amurka na gudanar da wasu ayyuka daga filin jirgin sama na Bauchi. Wannan na daga cikin hadin gwiwar tsaro tsakanin kasashen biyu.

Rahotanni sun nuna cewa Amurka na amfani da jiragen MQ-9 drones tare da sojoji kusan 200 a Najeriya.

Ayyukansu sun hada da horaswa da kuma bayar da bayanan sirri ga sojojin Najeriya da ke yaki da ‘yan ta’adda.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 3   +   7   =