Yayin da a baya-bayan nan gwamnonin jam’iyyun adawa ke tururwar komawa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, ita ma sabuwar haɗakar ADC ta yi gagarumin kamu a majalisar dattawan ƙasar.
A farkon watan Yulin 2025 ne jiga-jigan hamayyar ƙasar suka amince da yin ƙawance a jam’iyyar ADC domin ƙalubalantar shugaba Tinubu na APC a zaɓen 2027.
Tun daga wancan lokacin ne ADC ta riƙa zawarcin manyan ƴansiyasa a ƙasar inda ɗaiɗaikun ƴansiyasa suka riƙa komawa cikinta.
Sai dai wannan mako ya kasance lokaci mafi nasara ga jam’iyyar bayan da ƴanmajalisar dattawa tara suka sanar da komawa cikinta, wanda suka kasance masu riƙe da muƙamai mafiya yawa da suka shiga jam’iyyar a lokaci ɗaya.
Matakin na zuwa ne bayan a ƙarshen makon da ya gabata tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi ya sanar da komawa jam’iyyar a hukumance.
Sanatocin – waɗanda suka fito daga jam’iyyu daban-daban sun sanar da matakin ta bakin shugaban majalisar dattawan ƙasar, a lokacin zaman majalisar na makon.
Waɗanne sanatocin ne suka sanar da wannan mataki?