Kamfanin mai na TotalEnergies sun bayyana a shafinsu na masu zuba jari cewa yakin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran zai rage yawan man da kamfanin ke hakowa a duniya da kusan kashi 15 cikin dari.
Kamfanin ya ce rikicin da ya kara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya ne ya sa ake fuskantar wannan raguwar samar da mai.
Kamfanin na Faransa ya kuma bayyana cewa ya dakatar ko kuma yana shirin dakatar da aiki a wasu wuraren hakar mai a yankin, ciki har da wurare a Qatar da Iraq, da kuma filayen mai da ke cikin teku a Hadaddiyar Daular Larabawa, saboda karuwar tashin hankali na soji a yankin.