Home WassanniMan U ta ƙwallafa rai kan Lopez, Juventus na zawarcin Rudiger

Man U ta ƙwallafa rai kan Lopez, Juventus na zawarcin Rudiger

Kungiyoyin Manchester City da Manchester United na son ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Italiya Tonali mai shekara 25 daga Newcastle, duk da cewa tsohon ɗan wasan AC Milan ya fi son komawa ƙasarsa. (Talksport)

236 views

Kungiyoyin Manchester City da Manchester United na son ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Italiya Tonali mai shekara 25 daga Newcastle, duk da cewa tsohon ɗan wasan AC Milan ya fi son komawa ƙasarsa. (Talksport)

An ce White na iya komawa cikin tawagar Ingila, amma akwai yiwuwar ya bar Arsenal a bazara, inda Everton ke zawarcinsa. (FourFourTwo)

Aston Villa na cikin kungiyoyin Premier League da ke duba yiwuwar daukar matashin ɗan wasan gaba na Paris Saint-Germain, Ibrahim Mbaye mai shekara 18 a bazara. (Sky Sports)

Manchester United ta saka sunan ɗan wasan baya na Fulham, Antonee Robinson mai shekara 28 cikin jerin ‘yan wasan da take son ɗauka (Football Insider)

West Ham United da Nottingham Forest za su fuskanci gasa daga AC Milan wajen neman ɗan wasan gaba na Bologna, Santiago Castro mai shekara 21. (Tuttomercatoweb)

Manchester United na shirye ta kashe har fam miliyan 86.5 domin ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Barcelona, Fermin Lopez, amma ɗan wasan mai shekara 22 ba ya son barin kungiyar. (El Chiringuito)

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 3   +   5   =