Home LabaraiKotu Ta Dage Sauraren Bukatar Belin Nasir El-rufai Zuwa Ranar 14 Ga Wata

Kotu Ta Dage Sauraren Bukatar Belin Nasir El-rufai Zuwa Ranar 14 Ga Wata

102 views

Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna ta dage sauraren bukatar belin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, har zuwa ranar 14 ga wannan wata.

 

Kotun ta bayyana hakan ne a zamanta na yau Laraba, bayan sauraron ɓangarorin da ke gabanta kan batun neman belin.

 

Alkalin kotun bai yanke hukunci kan bukatar belin a wannan zama ba, inda ya ce an dage sauraren karar domin bai wa kotu karin lokaci duba hujjoji da bayanan da aka gabatar.

 

Ana sa ran za a ci gaba da sauraron karar a ranar 14 ga watan, inda kotu za ta yanke matsaya kan bukatar belin tsohon gwamnan.

 

Lamarin na ci gaba da jan hankalin al’umma, musamman ma masu bibiyar harkokin siyasa da shari’a a Najeriya.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 0   +   3   =