Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta sanar da ceto mutum biyar da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a kan hanyar Anka zuwa Bukuyum.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun tare matafiyan ne tare da tafiya da su zuwa cikin daji. Bayan samun bayanan sirri, jami’an ’yan sanda suka bi sawun maharan har zuwa maboyarsu.
An yi musayar wuta tsakanin jami’an tsaron da ’yan bindigar, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa tare da barin mutanen da suka sace.
Jami’an sun yi nasarar kubutar da dukkan mutanen biyar ba tare da sun samu rauni ba. Haka kuma, sun kwato babura biyu da ake zargin maharan na amfani da su wajen aikata laifuka.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Yazid Abubakar, ya ce rundunar za ta ci gaba da gudanar da samame domin yaki da ayyukan ’yan ta’adda a fadin jihar.
Ya kuma bukaci al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai tare da gaggauta kai rahoton duk wani motsi da ake zargi.