NDC ta bayyana Mustapha Kwankwaso a matsayin mataimakin ɗan takarar gwamnan Kano
Jam’iyyar NDC ta zaɓi Mustapha Rabiu Kwankwaso a matsayin mataimakin ɗan takarar gwamna a Kano domin zaɓen shekarar 2027.
Ɗan takarar gwamnan jam’iyyar, Aminu Abdussalam Gwarzo, shi ne ya sanar da matakin.
Mustapha Kwankwaso ya taba zama kwamishinan wasanni na jihar Kano a shekarar 2023, kafin daga bisani ya sauka daga muƙamin a 2026.
Hadimin Rabiu Musa Kwankwaso, Saifullahi Hassan, ya tabbatar da batun ta shafinsa na Facebook.
Rahotanni sun ce an cimma matsayar ne bayan wata ganawa ta musamman da masu ruwa da tsaki suk
a gudanar.