Jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP) ta zargi tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da sayen fom ɗin takara na kujeru 69 a jihar domin zaɓen shekarar 2027.
Shugaban Masu Ruwa da Tsaki na Shiyyar Arewa maso Yamma na jam’iyyar, Abdulkadir Musa Guza, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Kano ranar Lahadi.
Guza ya ce an samu bayanan cewa mutum guda, wanda ba mamba ba ne a jam’iyyar, ya sayi fom ɗin tsayawa takara na dukkan kujerun da ke ƙarƙashin PRP a jihar.
Ya bayyana cewa lamarin na barazana ga dimokuraɗiyyar cikin gida ta jam’iyyu, tare da yiwuwar haddasa ruɗani da rikice-rikice a lokacin zaɓe.
A cewarsa, jam’iyyar ta damu da rahotannin da ke alaƙanta Kwankwaso da wannan mataki, yana mai cewa bai dace mutum ya rinƙa neman mallakar tikitin takara na jam’iyyu daban-daban ba.
Guza ya yi kira ga Sanata Kwankwaso da ya guji tsoma baki a harkokin cikin gidan PRP, yana mai gargadin cewa jam’iyyar za ta iya ɗaukar matakin shari’a domin kare mutuncinta da haƙƙin mambobinta idan aka ci gaba da abin da ta kira katsalandan.
Sai dai zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bai mayar da martani kan zarge-zargen da PRP ta yi masa ba.