Tsohon kwamishinan kasuwanni na jihar Kano kuma jigo a tafiyar Kwankwasiyya, Alhaji Shehu Wada Sagagi, ya bayyana cewa an kai wani mataki mai nisa na shirin shigar jagoran tafiyar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, cikin sabuwar jam’iyyar NDC.
Sagagi ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan halin da ake ciki a jam’iyyar ADC, inda ya ce rikice-rikicen cikin gida da kuma shari’o’in da ke gaban kotuna daban-daban na iya zama babban cikas ga nasarar jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027.
A cewarsa, “halin da ADC ke ciki yanzu na nuna cewa akwai buƙatar neman wata mafita mai ɗorewa, domin tabbatar da an ci gaba da tafiyar siyasa cikin kwanciyar hankali da nasara.”
A wani ɓangare kuma, rahotanni na nuni da cewa ana shirin ganin haɗin gwiwa tsakanin Sanata Kwankwaso da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, a ƙarƙashin jam’iyyar NDC.
Majiyoyi sun ce ana sa ran su fito takara tare a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa, inda ake hasashen tikitin haɗin gwiwa na Obi–Kwankwaso zai iya zama ɗaya daga cikin manyan zaɓuɓɓuka a siyasar Najeriya gabanin 2027.
Sai dai har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga ɓangarorin da abin ya shafa dangane da wan
nan shiri.