Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yaba wa Masarautar Saudiyya bisa bayar da guraben karatu na cikakken tallafi ga daliban Najeriya 50 a fannin nazarin man fetur da ma’adinai, tana mai bayyana hakan a matsayin babban jari ga ci gaban ƙwarewar matasan ƙasar da kuma ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kai na Kasa, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi jakadan Saudiyya a Najeriya, Yousef Bin Mohammed Al-Balawi, a wata ziyarar girmamawa da ya kai ofishinsa da ke Abuja a ranar Litinin, 27 ga Afrilu, 2026.
Ministan ya bayyana godiyar Najeriya kan wannan shiri, yana mai cewa yana da matuƙar muhimmanci wajen inganta manyan fannoni na tattalin arziki kamar man fetur da ma’adinai. Ya ce shirin zai taimaka wajen horar da ƙwararrun ma’aikata da za su tallafa wa ci gaban tattalin arzikin ƙasa.
Ya kuma bayyana cewa ana sa ran shirin zai kasance mai dorewa, inda a kowace shekara dalibai 50 za su ci gajiyar tallafin, abin da zai tabbatar da ci gaba da samun ƙwararru a fannin.
Haka kuma, Ministan ya tabbatar wa jakadan Saudiyya ƙudirin Najeriya na ƙarfafa dangantakar diflomasiyya da kuma hanzarta aiwatar da yarjejeniyoyin da ake da su tsakanin ƙasashen biyu.
A nasa bangaren, Jakada Al-Balawi ya bayyana godiyar gwamnatin Saudiyya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa nuna goyon baya, yana mai cewa hakan yana nuna ƙarfafan dangantaka tsakanin ƙasashen.
Ya ce tallafin karatun ya haɗa da kuɗin makaranta, tikitin tafiya, masauki da kuma alawus na wata-wata, yana mai jaddada cewa shirin saka jari ne a makomar matasan Najeriya.
An gudanar da taron ne tare da halartar manyan jami’an ma’aikatar yada labarai da wasu manyan jami’ai na gwamnati.
