Gwamnatin Tarayya ta musanta rahotannin da ke cewa tana shirin ƙaƙaba sabbin haraji kan harkokin sadarwa da man fetur, bayan wata shawara da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya bayar a rahotonsa na baya-bayan nan kan tattalin arzikin Najeriya.
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Kuɗi ta fitar, gwamnatin ta bayyana cewa shawarwarin da IMF ke bayarwa ba doka ba ne kuma ba su zama manufofin gwamnatin Najeriya kai tsaye ba.
Sanarwar ta jaddada cewa babu wani shiri na ƙara haraji a ɓangaren sadarwa ko na man fetur. Ta kuma bayyana cewa duk wani sauyi da ya shafi haraji dole ne ya bi hanyoyin doka da majalisa tare da la’akari da bukatun ƙasa da yanayin tattalin arziki.
Gwamnatin ta ƙara da cewa har yanzu rangwamen Harajin Ƙarin Daraja (VAT) kan kayayyakin man fetur yana nan daram, kuma ba a soke shi ba. Haka kuma, duk da cewa doka ta tanadi yiwuwar sanya ƙarin kuɗi kan man fetur, hakan ba zai fara aiki ba sai an fitar da umarnin minista tare da wallafa shi a jaridar gwamnati, abin da ta ce ba a la’akari da shi a halin yanzu.
Dangane da fannin sadarwa, gwamnatin ta ce harajin excise duty da aka ƙaddamar kafin shekarar 2023 an riga an soke shi ƙarƙashin sabbin dokokin haraji, saboda haka ba ya aiki yanzu.
Gwamnatin Tarayya ta bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da rahotannin da ke ikirarin cewa ana shirin ƙara haraji kan sadarwa da man fetur. Ta tabbatar da cewa tana mai da hankali ne wajen aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki, inganta tattara kuɗaɗen shiga, jawo hannun jari da samar da ayyukan yi, maimakon ɗora wa al’umma sabbin nauyin haraji.
Ta kuma tabbatar da cewa duk wani matakin haraji da za a ɗauka nan gaba za a sanar da jama’a ta hanyoyin gwamnati da suka dace kuma bisa t
anadin doka.