
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kaddamar da sabon dandamalin Digital Switch Over (DSO), wanda zai bai wa ‘yan Najeriya damar kallon talabijin ta hanyar fasahar zamani kyauta, tare da hasashen samar da guraben ayyukan yi da bunƙasa masana’antar shirye-shiryen talabijin da tattalin arziki gaba ɗaya.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ƙasa, Mohammed Idris, ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da shirin a hedikwatar NIGCOMSAT da ke Abuja. Ya ce shirin wani muhimmin mataki ne na zamani domin inganta harkokin watsa shirye-shirye a Najeriya, tare da tallafa wa manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na sauyin fasahar zamani da bunƙasa tattalin arziki.
Ministan ya ce cikakken aiwatar da tsarin DSO zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, ƙarfafa masana’antun cikin gida, faɗaɗa kasuwar masu kallo, ƙara damar talla, da samar da sababbin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ga gidajen rediyo da talabijin da masu shirya shirye-shirye.
Mohammed Idris ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta maye gurbin wata fasaha da wata ba ne, sai dai tana ƙara hanyoyin isar da shirye-shiryen talabijin ta hanyar haɗa tsarin Digital Terrestrial Television (DTT), tauraron dan adam (Satellite) da kuma dandamalin zamani na intanet.
A nasa jawabin, Ministan Sadarwa, Kirkire-kirkire da Tattalin Arzikin Zamani, Dr. Bosun Tijani, ya ce DSO wani muhimmin bangare ne na shirin gwamnatin Tinubu na gina tattalin arzikin zamani mai darajar dala tiriliyan ɗaya. Ya kuma bayyana shirye-shiryen shimfiɗa kilomita dubu 90 na fiber-optic da ƙaddamar da sabbin tauraron dan adam guda biyu domin inganta sadarwa a ƙasar.
Shi ma Darakta Janar na Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Kasa (NBC), Charles Ebuebu, ya ce sabon dandamalin ba talabijin kaɗai ba ne, har ma wata babbar kafa ce da za ta faɗaɗa damar samun bayanai, ilimi da sauran damar zamani ga al’umma.
A nata ɓangaren, Shugabar NIGCOMSAT, Jane Egerton-Idehen, ta ce tsarin zai taimaka wajen cike gibin sadarwa, ƙarfafa masana’antar kirkire-kirkire da samar da damammaki ga masu shirya shirye-shirye, masu zuba jari da masana’antun fasaha.
Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Benjamin Kalu, ya bayyana ƙaddamar da shirin a matsayin babban nasara ta ƙasa, yana mai cewa zai ƙara samar da ayyukan yi, jawo hannun jari da bunƙasa harkokin yaɗa labarai da masana’antar kirkire-kirkire.
Sabon dandamalin DSO na daga cikin matakan gwamnatin tarayya na amfani da fasahar zamani wajen inganta sadarwa da samar da sabbin damar tattalin arziki ga ‘yan Najeriya.