
Ƙungiyar Manoman Koko da Ayaba ta Najeriya (CPFAN) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da su tura masu gadin dazuka zuwa yankunan gonaki domin kare manoma daga hare-haren ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.
Mataimakin Shugaban Ƙungiyar na Kudu maso Gabas, Samuel Dickson, ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro na ci gaba da tilasta wa manoma da dama barin gonakinsu saboda fargabar hare-hare.
Dickson ya ce ba za a iya cimma burin samar da wadataccen abinci a Najeriya ba, muddin manoma ba su da tabbacin tsaro a yankunan da suke noma.
Ya ƙara da cewa, maimakon a jibge masu gadin dazuka a manyan tituna, ya kamata a tura su cikin dazukan da manoma ke gudanar da ayyukansu domin tabbatar da tsaron gonaki.
Har ila yau, ya koka kan matsalolin ƙarancin kayan aikin noma da kuma rashin isassun kuɗaɗen gudanar da harkokin noma, yana mai cewa waɗannan na daga cikin manyan ƙalubalen da ke hana bunƙasar fannin noma a ƙasar.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da su ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin manoma tare da zuba jari a fannin noma, domin tabbatar da wadatar abinci da bunƙasar tattalin arzikin ƙasa.