Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da ƙara alawus-alawus na tafiye-tafiye ga ma’aikatanta da kaso 100.
Sanarwar ta ce, wannan ƙarin zai shafi dukkan ma’aikatan gwamnati da aikin hukuma ya kai su wajen ofis, ba tare da la’akari da inda suka dosa ba.
Haka kuma, gwamnatin ta bayyana cewa ta tanadi ƙarin alawus ɗin kama masauki ga ma’aikatan da suka yi tafiya saboda aikin gwamnati.
A wani bangare kuma, an bullo da sabon tsari na bai wa ma’aikata masu ritaya wani kunshin kuɗin sallama, wanda za a gudanar da shi ƙarƙashin hukumar kula da fansho.
Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Didi Walson-Jack, ta ce sabon tsarin ya tanadi bai wa ma’aikatan da za su yi ritaya cikakken kaso 100 na albashinsu na shekara guda, domin nuna godiya ga gudunmawar da suka bayar ga ƙasa.
Ta ƙara da cewa, dukkan ma’aikatan gwamnatin tarayya za su amfana da wannan tsari, ba tare da la’akari da tsarin alba
shinsu ba.