An gudanar da wani taro na musamman a ranar Lahadi 19 ga watan Afrilu, 2026 domin gabatar da katin zama ɗan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ga Dr. Nasir Bashir Aminu a garin Zariya, jihar Kaduna.
A yayin taron, Shugaban MMRR na Jihar Kaduna, Ibrahim Sidi Bamalli, tare da Sakatariyar MMRR ta jihar, Hajiya Hafsat Baba, da wasu mambobi ne suka miƙa masa katin a hukumance.
An shirya taron ne ƙarƙashin jagoranci da gayyatar shugabannin MMR na mazabar Muchia, a ƙaramar hukumar Sabon Gari.
Taron ya samu halartar jama’a da dama, inda daruruwan magoya baya da al’ummar gari daga sassa daban-daban na Zariya da kewaye suka hallara domin shaida wannan gagarumin bi
ki.