Kungiyar masu hayar babura ta ƙaramar hukumar Sabon Gari da ke Zariya mai suna “Ina Mafita” ta gudanar da taron shugabanni da mambobinta domin tattauna muhimman tsare-tsare da za su inganta harkar sufurin babura tare da ƙarfafa tsaro a faɗin ƙaramar hukumar da Jihar Kaduna baki ɗaya.
A yayin taron, shugabannin ƙungiyar sun bayyana wasu muhimman kudurori da suka haɗa da samar wa dukkan mambobin ƙungiyar shaidar zama ɗan ƙungiya, rigunan T-shirt, stickers, fom ɗin rajista da sauran hanyoyin tantance mambobi domin inganta tsaro da kuma kawo tsari a harkar hayar babura.
Ƙungiyar ta bayyana cewa aiwatar da waɗannan tsare-tsare zai taimaka wa gwamnati wajen ƙara inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da bai wa fasinjoji kwarin gwiwar amfani da masu hayar babura wajen zirga-zirgar su ta yau da kullum zuwa kasuwanni, makarantu, asibitoci da sauran wurare.
Taron ya samu halartar dimbin shugabanni da mambobin ƙungiyar, ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙungiyar, Malam Hamisu Salisu (PTF Basawa), tare da Sakataren ƙungiyar. An gudanar da taron ne a unguwar Basawa da ke ƙaramar hukumar Sabon Gari, Jihar Kaduna.
