
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana ƙarancin masu zuwa karɓar katin zaɓe na dindindin (PVC) a jihohi da dama a ranar farko ta fara rabon katunan, gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa, duk da fara aikin cikin kwanciyar hankali a wurare da dama, wasu jihohi sun samu ƙarancin masu zuwa karɓar katunan, yayin da wasu suka fuskanci matsaloli sakamakon rashin jami’an INEC a cibiyoyin karɓar katunan.
A jihar Abia, wasu masu rajistar zaɓe sun nuna fushinsu bayan sun kasa karɓar katunansu saboda rashin jami’an hukumar a wasu cibiyoyi. Sai dai a Ogun, wasu masu zaɓe sun yaba da yadda aikin ya gudana cikin sauƙi.
INEC ta ce ƙarancin masu zuwa a ranar farko na iya kasancewa saboda sabon fara aikin, tana mai fatan adadin zai ƙaru a kwanakin da za su biyo baya.
Hukumar ta tsara gudanar da rabon katunan a matakin unguwanni daga ranar 9 zuwa 15 ga Oktoba, 2026, sannan a ci gaba da rabon a ofisoshin ƙananan hukumomi daga ranar 16 ga Oktoba.
Ta kuma buƙaci duk masu rajistar zaɓe da suka cancanta su gaggauta karɓar katunansu tare da duba sunayensu a rajistar masu zaɓe, domin tabbatar da shirinsu na shiga zaɓen 2027.