Daraktan shiyya na Hukumar Kula da Watsa Labarai ta Najeriya (NBC), reshen Kaduna, Alhaji Adamu Salihu, ya bukaci Nagarta Radio da ta ci gaba da bin ƙa’idojin da’a da ƙwarewa wajen gudanar da aikin jarida.
Alhaji Adamu Salihu ya bayyana hakan ne lokacin da ya jagoranci tawagar hukumar a wata ziyarar ban girma da suka kai ofishin Nagarta Radio.
Ya jaddada muhimmancin bin ƙa’idojin aikin jarida da kuma dokokin da suka shafi harkar yaɗa labarai, musamman a wannan lokaci na siyasa.
Daraktan ya kuma shawarci Radio Nagarta da ta riƙa adana bayanan duk shirye-shiryen siyasa da tallace-tallacen siyasa na tsawon kwanaki 150, domin ba da damar tantance su a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Alhaji Adamu Salihu ya ƙara jaddada buƙatar ci gaba da kyakkyawar alaƙa tsakanin Nagarta Radio da NBC, domin inganta harkokin watsa shirye-shirye da kuma tabbatar da bin dokoki da ƙa’idojin hukumar.
Da yake mayar da martani, Babban Manajan Nagarta Radio, Alhaji Nasiru Yakubu Birnin Yero, ya ce bin ƙa’idojin da’a na aikin jarida abu ne mai matuƙar muhimmanci, musamman a lokacin siyasa.
Alhaji Nasiru ya tabbatar wa NBC cewa Nagarta Radio za ta ci gaba da gudanar da rahotanninta da shirye-shiryenta bisa adalci, daidaito da kuma bai wa ɓangarori daban-daban damar bayyana ra’ayoyinsu.
Ya ce tashar rediyon a shirye take ta ci gaba da haɗin gwiwa da NBC tare da bin dokoki da ƙa’idojinta, domin tabbatar da watsa shirye-shiryen da ke wayar da kan jama’a, ilmantar da su da kuma haɗa kan al’umma.
Babban Manajan ya kuma yaba wa NBC bisa ci gaba da gudanar da shirye-shiryen wayar da kan kafafen yaɗa labarai da kuma jagorantar su kan dokoki da ƙa’idojin da suka shafi harkar wats
a shirye-shirye.