Home LabaraiGwamnatin Sokoto Ta Buƙaci Jama’a Su Ba Da Shawarwari Kan Kasafin Kuɗin 2027

Gwamnatin Sokoto Ta Buƙaci Jama’a Su Ba Da Shawarwari Kan Kasafin Kuɗin 2027

17 views

Gwamnatin Jihar Sokoto ta buƙaci al’ummar jihar da su bayar da shawarwari masu tasiri yayin da ake fara shirye-shiryen tsara kasafin kuɗin shekarar 2027.

Kwamishinan Kasafi da Ci gaban Tattalin Arziƙi na jihar, Dakta Bashir Muhammad Achida, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da taron tattaunawa da jama’a na yankin Kudu a garin Bodinga.

Dakta Achida ya ce taron na daga cikin ƙudirin Gwamna Ahmed Aliyu na tabbatar da mulki mai buɗe ido da bai wa jama’a damar shiga harkokin gudanar da gwamnati.

Ya bayyana cewa shawarwarin da aka samu daga jama’a a shekarar da ta gabata sun haifar da sakamako mai kyau, inda aka aiwatar da mafi yawan buƙatun da aka sanya cikin kasafin kuɗin shekarar 2026, yayin da ake dab da kammala sauran.

Kwamishinan ya kuma sanar da cewa, domin ƙara faɗaɗa damar jama’a na bayar da gudummawa, gwamnatin za ta kai irin waɗannan taruka zuwa dukkan ƙananan hukumomin jihar a shirye-shiryen kasafin kuɗin shekarar 2027.

A nasa jawabin, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Sokoto, Rt. Hon. Tukur Bala Bodinga, wanda Mataimakin Shugaban Masu Tsawatarwa na Majalisar, Hon. Abubakar Shehu Shamaki, ya wakilta, ya yaba da shirin, tare da alƙawarin ɗaukar matakin gaggawa kan kasafin kuɗin da zarar an miƙa shi ga majalisa.

Sauran masu ruwa da tsaki, ciki har da Babban Sakataren Ma’aikatar, Buhari Umar, Shugaban Ƙungiyar Ƙananan Hukumomi ta Najeriya (ALGON) a jihar, Alhaji Abba Shehu Tambuwal, da wakilin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Dagacin Sifawa, sun bayyana taron a matsayin wata muhimmiyar dama da za ta bai wa jama’a damar taka rawa wajen tsara kasafin kuɗi.

Ƙungiyoyin fararen hula, mata da masu buƙata ta musamman, da kuma shugabannin gargajiya da na addini sun halarci taron, tare da matasa da sauran masu ruwa da tsaki.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 5   +   6   =