Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce gwamnatinsa ba za ta taɓa shiga tattaunawa da ƴan bindiga ba, yana mai jaddada cewa za a ci gaba da ɗaukar matakan soji har sai sun miƙa wuya ko kuma su fuskanci hukunci bisa doka.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin Babban Ma’aikacin Fadar Gwamnatin jihar, Alhaji Mukhtar Musa, yayin ƙaddamar da sakatariyar Ƙungiyar ‘Yan Asalin Jihar Zamfara Mazauna Kaduna, a ranar Lahadi.
A cewarsa, gwamnatin Gwamna Dauda Lawal na ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da jami’an tsaro domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a jihar.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da samar wa jami’an tsaro kayan aiki, kayan tallafi, alburusai da sauran abubuwan da za su ƙarfafa ayyukansu wajen yaƙi da masu aikata laifuka.
Mukhtar Musa ya ce, “Gwamnan ba zai taɓa yin sulhu da ƴan bindiga ba. Duk wanda yake son miƙa wuya ya yi hakan, in ba haka ba zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.”