Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya ce ba zai janye wa ɗan takarar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ba a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Obi ya bayyana cewa batun haɗa kai tsakanin shi da Atiku yanzu ya wuce matakin mutum ɗaya, domin kowannensu ɗan takara ne a ƙarƙashin wata jam’iyya. Ya ce duk wata yarjejeniya ko haɗin gwiwa dole ne ta kasance tsakanin jam’iyyun siyasa da ke da hannu a shirin.
A wata hira da gidan talabijin na Arise TV, Obi ya kuma musanta cewa ya taɓa ƙin amincewa da tayin zama mataimakin Atiku. Ya ce bai taɓa kasancewa cikin wani yanayi da aka miƙa masa irin wannan tayin ba.
Obi ya ce idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa, ba zai soke tsarin shawagi na darajar Naira ba, sai dai zai mayar da hankali wajen ƙara samar da kayayyaki da bunƙasa tattalin arziki domin ƙarfafa darajar kuɗin ƙasar. Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su guji ƙabilanci a zaɓen 2027.
Dan takarar NDC ɗin ya kuma ce shugaban ƙasa bai kamata ya riƙa yin hutunsa a ƙasashen waje ba. Ya ce idan ya zama shugaban ƙasa, zai riƙa yin hutunsa a Najeriya tare da ziyartar jihohin da ke fama da matsalar tsaro da sauran ƙalubale domin fahimtar halin da al’umma ke ciki.