Hukumar Zaɓe ta Ƙasa mai Zaman Kanta (INEC) ta sanar da ƙara wa’adin ci gaba da rajistar masu zaɓe na tsawon makonni biyu, domin bai wa ‘yan Najeriya da suka cancanta ƙarin damar yin rajista.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Hukumar, Mohammed Kudu Haruna, ya sanya wa hannu, INEC ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bayan nazarin yadda aikin rajistar ke gudana, tare da la’akari da shawarwari da ra’ayoyin da ta samu daga ofisoshinta na jihohi, jam’iyyun siyasa, ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki.
Hukumar ta bayyana cewa aikin rajistar, wanda ya fara a ranar 18 ga Agustan 2025, kuma aka tsara kammala shi a ranar 10 ga Yulin 2026, yanzu zai ci gaba har zuwa ranar Lahadi, 26 ga Yulin 2026.
Haka kuma, INEC ta sanar da ƙaddamar da tsarin rajistar masu zaɓe ta intanet ga masu yin rajista karo na farko.
A cewar hukumar, daga ranar 8 ga Yulin 2026, sabbin masu rajista za su iya shiga shafinta na intanet domin fara da kuma kammala matakan rajistarsu cikin sauƙi.