Gwamna Ahmed Aliyu na jahar Sokoto ya ce shekara uku yana rabawa manoma taki kyauta, amma saboda masu kokarin karkatar da takin, bana mun sauya tsari za a biya wani dan kaso don takin ya kai ga manoma na gaskiya.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta ɗauki sabbin matakai domin dakile karkatar da takin, yana mai cewa idan an yi nasarar kawar da wannan matsala, za a ci gaba da rabon taki kyauta ga manoma.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnati ta sayo buhunan ingantattun iri 12,800 da suka haɗa da gero, masara, wake, dawa da shinkafa ta FARO 44, tare da magungunan kashe ciyawa da kwari domin rabawa manoma.
A wani mataki na bunƙasa aikin noma, Ahmed Aliyu ya ce gwamnatin jihar ta sayo taraktocin Massey Ferguson MF-375 guda 250 kan kuɗi sama da naira biliyan 22.1, inda aka riga aka biya kashi 75 cikin 100 na kuɗin kwan
gilar.