Home LabaraiMutum 18 Sun Rasu a Rikicin Manoma da Makiyaya a Neja

Mutum 18 Sun Rasu a Rikicin Manoma da Makiyaya a Neja

16 views

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta tabbatar da cewa mutum 18 sun rasa rayukansu sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a Ƙaramar Hukumar Rafi ta jihar.

Kakakin rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya ce rikicin ya fara ne a ranar 29 ga watan Yuni, sannan ya tsananta bayan hare-haren ramuwar gayya. Ya bayyana cewa mutane 15 sun ƙone ƙurmus a wani gida da ke Anguwan-Baago, yayin da wasu uku suka mutu a wasu hare-hare daban.

’Yan sanda sun ce ana kyautata zaton rikicin na da alaƙa da tsohuwar taƙaddama kan mallakar ƙasa, kuma an tura jami’an tsaro zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya.

Sai dai wasu mazauna yankin sun ce adadin waɗanda suka mutu ya fi abin da ’yan sanda suka bayyana, tare da zargin cewa hare-haren sun ci gaba har zuwa ranar Alhamis.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 8   +   3   =