Home LabaraiDalilin shirya taron Haɗin Kai Domin Magance Rashin Tsaro a Arewacin Nijeriya – ACI

Dalilin shirya taron Haɗin Kai Domin Magance Rashin Tsaro a Arewacin Nijeriya – ACI

25 views

Darakta Janar na ƙungiyar Arewa Cohesion for Peace, Unity and Development Initiative (ACI), Dakta Abdullahi Idris, ya ce manufar shirya taron wayar da kai na Arewa kan matsalar rashin tsaro ita ce samar da hanyoyin magance matsalolin tsaro cikin gaggawa da kuma samar da mafita mai ɗorewa.

 

Dakta Abdullahi Idris ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna gabanin taron wayar da kan, wanda aka shirya gudanarwa a ranar Laraba mai zuwa.

 

A cewarsa, yankin Arewa ya shafe shekaru da dama yana fuskantar manyan ƙalubalen tsaro, lamarin da ya janyo raba iyalai da muhallansu, durƙusar da harkokin tattalin arziki, tare da barazana ga zaman lafiya da haɗin kan al’ummomin yankin.

 

Ya ce domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa a Arewa, akwai buƙatar dukkan masu ruwa da tsaki su haɗa kai wajen samar da mafita, domin gwamnati kaɗai ba za ta iya magance matsalar ba.

 

Darakta Janar ɗin ya ƙara da cewa, wannan ne ya sa ƙungiyar Arewa Cohesion for Peace, Unity and Development Initiative (ACI) ta shirya taron wayar da kai na Arewa mai taken “Haɗin Kai Domin Magance Rashin Tsaro a Arewacin Nijeriya”, domin haɗa kan al’umma da masu ruwa da tsaki wajen tattauna hanyoyin samar da zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a yankin.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 0   +   4   =