Home LabaraiJihohi Sun Fi Samun Kuɗi A Mulkin Tinubu — Gwamna Ahmed Aliyu

Jihohi Sun Fi Samun Kuɗi A Mulkin Tinubu — Gwamna Ahmed Aliyu

6 views

Jihohi Sun Fi Samun Kuɗi A Mulkin Tinubu — Gwamna Aliyu

Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya ce jihohi yanzu suna samun ƙarin kuɗaɗe daga Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda hakan ke ba su damar gudanar da ayyukan ci gaba da tallafa wa al’umma.

Gwamnan ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da sayar da kayan abinci a farashi mai rahusa a Bodinga, inda ya ce ingantattun kuɗaɗen da jihar ke samu ya taimaka wajen gudanar da ayyuka da kuma biyan albashi a ranar 18 ga kowane wata.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Sokoto da su goyi bayan Shugaba Tinubu a zaɓen 2027, tare da yabawa manufofinsa na tattalin arziki.

Dangane da tsaro, Gwamna Aliyu ya ce gwamnatinsa na tallafa wa jami’an tsaro, ciki har da samar da motoci masu sulke 62, sama da motocin sintiri 200 da babura 2,000.

Ya bukaci jama’a da su bai wa jami’an tsaro bayanai kan masu taimaka wa ’yan bindiga, tare da yin addu’ar kawo ƙarshen rashin tsaro a jihar da ƙasar baki ɗaya.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 9   +   6   =