Gwamnatin Jihar Sakkwato ta rabawa hukumomin tsaro motoci na aiki domin ƙarfafa yaƙi da ƴan bindiga da sauran ayyukan ta’addanci a faɗin jihar.
Mataimakin Gwamnan Jihar, Alhaji Idris Mohammed Gobir, wanda ya miƙa makullan motocin ga hukumomin tsaron, ya ce gwamnatin Gwamna Ahmed Aliyu ta samar da motocin ne domin inganta ayyukan jami’an tsaro da ƙarfafa tsarin tsaro a jihar.
Ya buƙaci hukumomin tsaron da su yi amfani da motocin yadda ya dace domin cimma manufar da aka samar da su.
Haka kuma, Alhaji Idris Mohammed Gobir ya jaddada cewa tabbatar da tsaro alhakin kowa ne, inda ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro haɗin kai ta hanyar kai rahoton duk wani abu ko mutum da ake zargi domin ɗaukar matakin da ya
dace.