Home LabaraiMinistan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci ’Yan Najeriya Su Guji Ƙin Fita Zaɓe a 2027

Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci ’Yan Najeriya Su Guji Ƙin Fita Zaɓe a 2027

14 views

 

 

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Ƙasa, Mohammed Idris, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su guji ƙin fita zaɓe, sayen ƙuri’u da rikicin siyasa gabanin babban zaɓen 2027.

 

Idris ya bayyana cewa ’yan ƙasa masu cancantar zaɓe na da alhakin kare dimokuraɗiyya ta hanyar shiga zaɓe cikin lumana, yana mai cewa sayar da ƙuri’u da tashin hankali na iya kawo cikas ga tsarin dimokuraɗiyya.

 

Ministan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mataimakinsa kan harkokin yaɗa labarai, Rabiu Ibrahim, ya fitar bayan ƙaddamar da shirin wayar da kan jama’a na Hukumar Wayar da Kan Ƙasa (NOA) a faɗin ƙasar gabanin zaɓen 2027.

 

A nasa ɓangaren, Darakta-Janar na NOA, Lanre Issa-Onilu, ya ce hukumar za ta yi amfani da harsunan gida, shirye-shiryen rediyo, tattaunawar al’umma da kafafen sadarwa na zamani wajen ƙarfafa fitowar masu zaɓe da hana sayen ƙuri’u. Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya kuma jaddada aniyar gudanar da zaɓe cikin gaskiya, adalci da sahihanci a 2027.

 

 

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 7   +   6   =