Home LabaraiSERAP Ta Buƙaci INEC Ta Yi Bayanin Yadda Aka Kashe Naira Biliyan 126 Na Kuɗaɗen Zaɓe

SERAP Ta Buƙaci INEC Ta Yi Bayanin Yadda Aka Kashe Naira Biliyan 126 Na Kuɗaɗen Zaɓe

3 views

Ƙungiyar kare haƙƙin jama’a da neman gaskiya, SERAP, ta maka Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa zargin gazawar hukumar wajen yin cikakken bayani kan yadda aka kashe sama da naira biliyan 126.46 da aka ware domin gudanar da ayyukan zaɓe.

 

A cikin ƙarar, SERAP ta buƙaci kotu ta tilasta wa INEC bayyana yadda aka kashe kuɗaɗen, waɗanda aka ware domin sayen kayan zaɓe, na’urori, motoci da sauran hidimomin da suka shafi gudanar da zaɓe. Ƙungiyar ta ce zarge-zargen sun fito ne daga rahoton binciken kuɗaɗen gwamnati na 2023 da Babban Mai Binciken Kuɗaɗen Tarayya ya wallafa a ranar 7 ga Agusta, 2026.

 

Rahoton ya yi zargin cewa an biya sama da naira biliyan 112 ba tare da bin ƙa’idojin sayen kayayyaki da hidimomin gwamnati ba, tare da nuna cewa babu hujjar da ke tabbatar da cewa an sayi kayayyakin da aka biya kuɗinsu. Haka kuma, an yi zargin cewa an biya sama da naira biliyan ɗaya domin sayen motocin Toyota Prado TXL na shekarar 2021 ba tare da bin wasu matakan da doka ta tanada ba.

 

SERAP ta kuma yi zargin cewa an biya sama da naira biliyan uku ga ’yan kwangila huɗu kafin bayar da kwangilolin, yayin da aka biya sama da naira biliyan tara kan kwangiloli 22 masu kama da juna, waɗanda rahoton ya ce wataƙila an rarraba su domin kauce wa ƙa’idojin sayen kayayyakin gwamnati. Ƙungiyar ta buƙaci INEC ta bayyana sunayen ’yan kwangila da jami’an da suka amince da waɗannan mu’amaloli, tare da gabatar da hujjojin cewa an samar da kayayyakin da aka biya kuɗinsu.

 

SERAP ta ce ’yan Najeriya na da haƙƙin sanin yadda ake kashe kuɗaɗen gwamnati, musamman waɗanda aka ware domin gudanar da zaɓe mai inganci. Ta kuma buƙaci kotu ta umarci INEC da ta kiyaye kayan zaɓe da sauran kadarorin gwamnati da rahoton ya ambata, domin kada a lalata su ko a sauya musu matsuguni ta yadda hakan zai kawo cikas ga bincike. Har yanzu dai ba a sanya ranar sauraron ƙarar ba.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 6   +   5   =