An yi kira ga al’ummar Najeriya da su rungumi al’adar kafa ƙungiyoyin taimakon kai da kai a garuruwa da unguwanninsu domin haɗa kai wajen magance matsalolin da ke addabar al’umma.
Wannan kiran ya fito ne daga Alhaji Balarabe Idris Jaji, wanda ya bayyana cewa kafa irin waɗannan ƙungiyoyi zai ƙarfafa haɗin kai tsakanin jama’a tare da samar da ci gaba mai ɗorewa a matakin al’umma.
Ya ce ƙungiyoyin za su kuma taimaka wa gwamnati da hukumomin da abin ya shafa wajen gudanar da ayyukansu cikin sauƙi da inganci, musamman a fannoni da suka shafi ci gaban al’umma da walwalar jama’a.
Alhaji Balarabe Idris Jaji ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, bisa ƙoƙarin da yake yi wajen inganta harkar kiwon lafiya da aiwatar da sauran ayyukan ci gaba a faɗin jihar. Ya bayyana cewa irin waɗannan matakai na gwamnati suna buƙatar cikakken goyon bayan al’umma domin samun ci gaba mai ɗorewa.