Home LabaraiAtiku Ya Bukaci Tinubu Ya Dakatar da Umahi Kan Mutuwar Mary Habila

Atiku Ya Bukaci Tinubu Ya Dakatar da Umahi Kan Mutuwar Mary Habila

7 views

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya umarci Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya ajiye muƙaminsa na wucin gadi har sai an kammala bincike kan mutuwar Mary Habila.

 

Atiku ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce dole ne a gudanar da bincike mai zaman kansa, gaskiya da kuma adalci domin gano musabbabin mutuwar Habila.

 

Mary Habila mai shekaru 26, ‘yar asalin Nok da ke Kudancin Kaduna, ta rasu ne a ranar 27 ga Yunin 2026 a wani gini da ke cikin gidan Ministan Ayyuka, David Umahi, a garin Uburu na Jihar Ebonyi.

 

Atiku ya ce ba ya zargin kowa da aikata laifi, amma ya jaddada cewa bincike mai inganci ne kaɗai zai tabbatar da gaskiya. Ya kuma nuna damuwa kan jinkirin gudanar da binciken tare da zargin cewa har yanzu ba a yi cikakken gwajin gawar (autopsy) ba.

 

Haka kuma, ya buƙaci Sufeto Janar na ‘Yan Sanda ya mayar da binciken zuwa Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sanda ta Ƙasa tare da haɗa ƙwararrun masana binciken kimiyyar shari’a (forensic experts), sannan a bayyana sakamakon binciken ga jama’a.

 

A nasa ɓangaren, Minista David Umahi ya riga ya buƙaci ‘yan sanda su gudanar da cikakken gwajin gawar tare da ƙwararrun likitocin bincike, kuma ya ce kada a miƙa gawar ga iyalanta har sai an kammala dukkan bincike.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 1   +   10   =