Al’ummomin Rigasa da Afaka sun fara aiwatar da matakan doka na neman ƙirƙirar sabuwar Ƙaramar Hukumar Rigasa, inda suka miƙa buƙatar neman amincewar Majalisar Ƙaramar Hukumar Igabi.
A cewar masu ruwa da tsakin, an haɗa kwamitoci da suka ƙunshi shugabannin gargajiya, dattawa, ‘yan siyasa, shugabannin addinai da matasa domin jagorantar wannan yunƙuri, wanda ake shirin kafa hedikwatar sabuwar ƙaramar hukumar a Sabon Afaka.
Kwamitin Tsaye na wannan aiki yana ƙarƙashin jagorancin Hon. Jabir Khamis Rigasa, yayin da Hon. Salisu A. Sulaiman Afaka ke matsayin Sakatare. Haka kuma, Alhaji Mu’azu Abubakar Ruma (Tafidan Afaka) ne ke jagorantar Kwamitin Dattawa, tare da Alhaji Ja’afar Dan Zaria Rigasa a matsayin Mataimakin Shugaba.
Masu ruwa da tsakin sun bayyana cewa matakin na daga cikin tsarin da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanada domin neman ƙirƙirar sabuwar ƙaramar hukuma.