Home LabaraiMummunan hari a Filato: ’Yan bindiga sun fille kan matashi a Bassa.

Mummunan hari a Filato: ’Yan bindiga sun fille kan matashi a Bassa.

178 views

matashi mai shekaru 30, Elisha Abbas Saku, ya rasa ransa bayan da ’yan bindiga suka kai hari tare da fille masa kai a ƙauyen Riwhie-Chwo da ke yankin Nzharuvo, Miango a Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato.

 

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren Alhamis, inda maharan suka kutsa cikin al’umma da misalin ƙarfe 10 na dare, lamarin da ya tayar da hankalin mazauna yankin.

 

Ƙungiyar Matasan Irigwe ta tabbatar da aukuwar harin, inda ta bayyana shi a matsayin mummunan ta’addanci tare da yin addu’ar Allah Ya jiƙan mamacin.

 

Hukumomin ’yan sanda a jihar ba su ce komai ba kan lamarin zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

 

Wannan na daga cikin jerin hare-haren da ke ci gaba da addabar wasu yankunan Jihar Filato, musamman Karamar Hukumar Bassa.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 5   +   9   =