Ministan albarkatun ruwa da tsafta Farfesa Joseph Terlumun Utsev, ya yi gargadi cewa garuruwa 14,118 a kananan hukumomi 266 a jihohi 33 hadi da Abuja na cikin hadarin fuskantar ambaliya a wannan shekara ta 2026.
Ministan ya bayyana hakan ne, a Fadar Shugaban Kasa a Abuja, ranar Laraba, yayin gabatar da rahoton shekara-shekara na bana a kan yanayin da za a iya fuskanta na ambaliya.
Taron ya gabatar hasashe da ke cike da shedu kan yuwuwar ambaliya, wanda hakan ya ba wa gwamnati da masu ruwa da tsaki da hukumomi da gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi da saurn al’umma domin su shirya tunkarar daminar bana kan yadda ambaliyar za ta iya kasancewa.
Matakan da za a dauka za su zama na kandagarkin samar da bayanai da wuri da kare rayukan da harkokin da jama’a ke rayuwa da su da kare kayayyakin amfanin jama’a da kuma rage illar da ambaliyar za ta iya yi ga harkokin tattalin a
rziki.