Home LabaraiGwamnatin Sokoto Ta Ninka Alawus ɗin Matasan NYSC a Jihar

Gwamnatin Sokoto Ta Ninka Alawus ɗin Matasan NYSC a Jihar

27 views

Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya amince da ƙara alawus ɗin da ake bai wa matasan da ke yiwa kasa hidima NYSC a jihar daga Naira 10,000 zuwa Naira 20,000 a kowane wata.

Haka kuma, gwamnan ya amince da bai wa matasa 1,523 da ke sansanin horaswa kyautar Naira 30,000 kowannensu, tare da bayar da sabuwar motar Hilux ga mai kula da shirin NYSC na jihar.

Ya kuma bayar da umarnin gyara ruwa da wutar lantarki a sansanin, tare da amincewa da yanka shanu biyar a kullum domin ciyar da matasan a lokacin horaswar.

Gwamnan ya kuma yi alƙawarin bayar da kyautar Naira miliyan ɗaya ga waɗanda suka lashe gasar tseren kada, yayin da waɗanda suka zo na biyu za su samu Naira 500,000.

Wannan na zuwa ne a yayin buɗe shirin horas da matasan NYSC na rukuni na C, kashi na biyu na shekarar 2026, a jihar Sakkwato.

Gwamna Aliyu ya jaddada aniyar gwamnatinsa na tallafa wa matasa da inganta jin daɗinsu da kuma tabbatar da zaman lafiya a jihar.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 2   +   9   =