Home KetareSaudiyya: Mutane 12 sun mutu, 309 sun jikkata a harin filin jirgin sama na Riyadh

Saudiyya: Mutane 12 sun mutu, 309 sun jikkata a harin filin jirgin sama na Riyadh

10 views

 

Mutane 12 sun mutu, yayin da wasu 309 suka jikkata sakamakon wani hari da aka kai filin jirgin saman King Khalid da ke birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, kawancen sojojin da Saudiyya ke jagoranta ya zargi ‘yan tawayen Houthi na Yemen da kai harin, tare da bayyana shi a matsayin babban laifin yaƙi.

Rahotanni sun ce harin ya tilasta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin, yayin da jami’an lafiya suka fara aikin ceto da kula da waɗanda suka jikkata, ciki har da wasu mahajjata da ke kan hanyarsu ta zuwa Makka.

A nasa ɓangaren, Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna yiwuwar ƙasarsa ta shiga aikin soji tare da Saudiyya domin kai hare-hare kan ‘yan Houthi, lamarin da ke ƙara tayar da fargabar faɗaɗar rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 6   +   9   =