Gwamnatin Amurka ta sanar da wani sabon sauyi a manufofin shige da ficen ƙasar, inda ta ce yawancin ƴan ƙasashen waje masu neman izinin zama na dindindin wato Green Card dole ne su fita daga Amurka kafin su gabatar da buƙatarsu a ofishin jakadancin Amurka.
Wani mai magana da yawun hukumar shige da fice ta Amurka ya bayyana cewa sabon tsarin zai taimaka wajen rage yawan masu neman izinin zama tare da sauƙaƙa korar waɗanda aka ƙi amincewa da buƙatarsu.
Sai dai lauyoyin shige da fice da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam sun nuna damuwa kan matakin, suna masu cewa dokar na iya haddasa rabuwar iyalai tare da jefa wasu cikin haɗari.
Sun ce sabuwar manufar na iya tilasta wa mutanen da suka tsere daga tashin hankali, fataucin mutane da sauran matsaloli komawa ƙasashen da suka gudu daga cikinsu domin kammala tsarin neman takardunsu.
Masu sukar matakin sun ce hakan na iya ƙara wahalar rayuwa ga bakin haure da iyalansu, yayin da gwamnatin ke cewa manufar na da nufin ƙarfafa dokokin shige da fice da kuma rage amfani da tsarin ba bisa ka’ida ba.