Shirin bunƙasa cigaban al’umma na jihar Katsina, wato Community Development Programme (CDP), na ci gaba da kawo sauyi a rayuwar al’ummomin karkara da masu rayuwa a lungu da saƙon jihar Katsina tun bayan ƙaddamar da shi da gwamnatin jihar ta yi a ƙarshen shekarar 2024.
A ranar 23 ga watan Nuwamban shekarar 2024 ne gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ƙaddamar da wannan shiri tare da damƙa ragamar jagorancinsa ga Kamaluddeen Kabir Katsina.
Tun daga farkon kafa shirin, jagorancin ofishin gudanarwa ya mayar da hankali wajen tabbatar da cewa al’umma sun samu damar bayyana matsalolinsu kai tsaye tare da jin manufofi da saƙonnin gwamnati ba tare da tangarɗa ba.
Domin cimma wannan buri, ofishin ya yi amfani da ma’aikatan ƙananan hukumomi da suka haɗa da jami’an cigaban al’umma, walwala da ilimi, wato CDO, CLO da CSO, inda aka ɗora musu nauyin zama masu haɗa gwamnati da al’umma. Haka kuma an ware musu alawus domin sauƙaƙa gudanar da ayyukansu a matakin gunduma.
Baya ga haka, an kafa kwamitocin cigaban al’umma a kowace gunduma domin kula da bukatun jama’a. Kwamitocin sun ƙunshi masu unguwanni da masu gari, limamai, dattawa, wakilan mata, matasa, ‘yan kasuwa da kuma masu buƙata ta musamman.
A wani mataki na ƙarfafa ayyukan shirin, gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Radda ta ware Naira miliyan goma ga kowace gunduma domin gudanar da ƙananan ayyuka da gyare-gyaren da al’umma suka fi buƙata.
An buɗe asusun banki na musamman domin kula da waɗannan kuɗaɗe ƙarƙashin kulawar kwamitocin gundumomi, inda duk wani aiki sai an tattauna tare da neman sahalewar ofishin gudanarwa kafin a fara aiwatar da shi.
Rahotanni daga sassa daban-daban na jihar na nuna cewa shirin ya taimaka wajen samar da ƙananan ayyukan more rayuwa tare da ƙara kusantar gwamnati da al’umma, musamman a yankunan karkara.
Masu lura da al’amura na ganin cewa nasarar da aka samu cikin ƙasa da shekaru biyu na da alaƙa da yadda aka gudanar da shirin bisa gaskiya, amana da kuma bai wa al’umma damar shiga cikin tafiyar cigaban yankunansu.
Ana sa ran a rubutu na gaba za a yi ƙarin bayani kan yadda shirin CDP ke taka rawa wajen isar da manufofi da saƙonnin gwamnati ga al’umma kai tsaye a fa
faɗin jihar Katsina.