Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya ce ana samun nasara a yaƙin da ake yi da rashin tsaro a jihar sanadiyyar sabon ƙoƙarin da ake yi wajen kawar da matsalar.
Gwamnan ya bayyana haka ne ranar Alhamis sa’ilin buɗe taron majalisar zartarwar jihar.
Aliyu ya ce “ina sanar da ku cewa sabon ƙoƙarin da muka fara yi na haifar da ci gaba, a yunƙurin da muke yi na kawar da ayyukan ƴan fashin daji da ke addabar ƙananan hukumomi 13”.
Gwaman ya ce ana kuma samun ci gaba a yaƙin da ake yi da sauran masu aikata laifuka a jihar.
Sokoto na cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da matsalar ƴan fashin daji.
Duk da iƙirarin da gwamnatoci ke yi, har yanzu abin ya ci tura, inda ƴan bindigar suka tarwatsa ƙauyuka da dama a jihar da ma wasu jihohin masu maƙwaftaka.
A cikin bayanin nasa, Ahmed Aliyu ya ce gwamnati na bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta “mayar da duk ƴan gudun hijira zuwa ƙauyukans
u na asali”.