’Yan bindiga sun sace Sakataren mulki na Karamar Hukumar Kibiya a Kano Hon. Hamza Musa Durba a daren Juma’a.
Kafar Arewa Updates ta rawaito cewa, Babban Jamiʼin Harkokin Tsaro na Karamar Hukumar Kibiya Malam Musa Hussaini Ibrahim ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce, maharan su 6 a kan babura ɗauke da bindigu sun shiga gidansa da ke garin Dinya a mazabar Durba inda suka yi awon gaba da shi.
A cewarsa, sun tarar da iyalansa a gidan amma ba su ɗauki kowa ba, kuma ba su yi ko harbi ba, sai suka sa shi a gaba suka tafi da shi.
Bayan faruwar lamarin tuni hukumomin tsaro suka shiga bincike da bin sahu don ceto shi.