Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya gargadi hakimai da dagatai a faɗin Masarautar Zazzau da su guji cin zarafi da zaluntar talakawa yayin gudanar da harkokinsu.
Gargadin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na Masarautar Zazzau, Abdullahi Aliyu Kwarbai, ya fitar bayan zaman majalisar masarautar ƙarƙashin jagorancin Sarkin Zazzau.
Majalisar ta warware wani rikicin rabon gado da ya shafi al’ummar Matarawa da ke Gundumar Kudan, inda aka yi zargin cewa wasu magada na gaskiya ba a ba su haƙƙinsu ba, yayin da wasu da ba su cancanta ba suka amfana daga rabon dukiyar mamacin.
Sanarwar ta ce wannan shi ne karo na uku da aka kawo ƙorafin gaban majalisar domin sasanci da sulhu.
Bayan gudanar da bincike da nazari, majalisar ta bayar da umarnin dakatar da dagacin ƙauyen da abin ya shafa tare da umartar a kwato dukkan kuɗaɗen da aka raba ba bisa ƙa’ida ba.
An kuma miƙa kuɗaɗen da aka kwato ga Sarkin Zazzau, wanda daga bisani ya damƙa su ga Hakiman Kudan da Hunkuyi domin sa ido kan sake rabon gadon cikin adalci da daidaito bisa tsarin shari’ar Musulunci.
Sarkin Zazzau ya jaddada cewa masarautar ba za ta lamunci duk wani nau’i na yaudara ko cin zarafin marasa ƙarfi ba.
Ya kuma buƙaci shugabannin gargajiya da su riƙa gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, adalci da riƙon amana domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’umma.
Majalisar Masarautar Zazzau ta sake tabbatar da aniyarta na amfani da tsarin sasanci da sulhu wajen magance rikice-rikicen al’umma da kare talakawa daga zalunci.