Home LabaraiGwamna Ahmed Aliyu ya tabbatar da ƙarin goyon baya ga ‘yan sandan Sakkwato.

Gwamna Ahmed Aliyu ya tabbatar da ƙarin goyon baya ga ‘yan sandan Sakkwato.

272 views

Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro domin yaki da ta’addanci da sauran nau’o’in laifuka a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yammacin ranar Laraba yayin da ya kai ziyara ga sabon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP), Olatunji Rilwan Disu, a ofishinsa da ke Abuja.

Ahmed Aliyu ya ce tun bayan hawansa mulki, gwamnatinsa ta samar da kayan aiki da sauran tallafi ga jami’an tsaro domin inganta kokarinsu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya kara da cewa daga farkon mulkinsa zuwa yanzu, gwamnati ta sayo tare da rabawa hukumomin tsaro motoci sama da 200 domin karfafa yaki da ta’addanci, musamman a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.

Gwamnan ya bayyana tsaro a matsayin babban ginshiki a cikin ajandarsa ta “9-Point Smart Innovative Agenda”, yana mai cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da hada kai da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Haka kuma, ya yabawa kokarin hukumomin tsaro wajen samun ci gaba duk da kalubalen ta’addanci, inda ya bukace su da su kara zage damtse tare da karfafa tattara bayanan sirri da musayar bayanai a tsakaninsu.

Gwamnan ya kuma bukaci a kara hada kai tsakanin hukumomin tsaro daban-daban domin samun nasara mai dorewa.

A nasa bangaren, Gwamna Aliyu ya yabawa tsohon Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Ahmed Musa, bisa gudunmawar da ya bayar wajen yaki da rashin tsaro, inda ya bayyana shi a matsayin jajirtaccen jami’i mai kwarewa da jajircewa.

Ya kuma bukaci sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda, Hayatu Hassan, da ya yi koyi da wanda ya gada ta hanyar nuna kwazo da rikon amana wajen gudanar da aikinsa.

Gwamnan ya taya sabon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda murna kan nada shi, tare da kira gare shi da ya tabbatar da amincewar da aka ba shi.

A nasa jawabin, sabon IGP, Olatunji Rilwan Disu, ya yabawa Gwamna Aliyu bisa irin goyon bayan da yake bai wa hukumomin tsaro, yana mai tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda za ta ci gaba da hada kai da gwamnatin jihar domin tabbatar da zaman lafiya a Sokoto.

Ya kuma gode wa gwamnan bisa wannan ziyara.

Gwamnan ya samu rakiyar Sakataren Gwamnatin Jihar, Muhammad Bello Sifawa, da kuma Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati, Aminu Haliru Dikko, mni.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 1   +   2   =