
Gwamnan Jihar Sokoto, Dr. Ahmed Aliyu, ya gargadi masu tukin kwale-kwale a Karamar Hukumar Goronyo kan yin lodin da ya wuce kima, tare da umartar hukumomin da abin ya shafa da su tsaurara matakan tsaro domin kauce wa sake asarar rayuka a hanyoyin ruwa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai garin Gorau da ke Goronyo, biyo bayan hatsarin kwale-kwale da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama. Wakilin gwamnan, Jagoran APC na jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya bayyana cewa kare rayuka da dukiyoyin al’umma na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin jihar ta sa a gaba.
A yayin ziyarar, tawagar gwamnatin ta kuma je Dinawa, Birjingo da Tsamaye domin jajanta wa al’ummomin da hare-haren ‘yan bindiga suka shafa, ciki har da mutuwar mutane bakwai a Dinawa da kuma rasuwar Shugaban APC na yankin, Abdullahi Yarima. Mataimakin Gwamnan Jihar, Engr. Idris Muhammad Gobir, da Sakataren Gwamnatin Jihar, Muhammad Bello Sifawa, sun sake tabbatar da aniyar gwamnati ta karfafa tsaro da kare rayukan al’umma.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Muhammad Bello Sifawa, ya kuma sanar da bayar da kayan abinci tare da tallafin Naira miliyan daya ga kowane daga cikin iyalan mutane 65 da suka rasu sakamakon hatsarin kwale-kwalen da hare-haren ‘yan bindiga. Ya ce tallafin na da nufin rage radadin da iyalan ke ciki da kuma nuna goyon bayan gwamnati a lokacin bakin ciki, yayin da aka gudanar da addu’o’i na musamman ga wadanda suka rasu.