Home WassanniIna Salah zai koma idan ya bar Liverpool?

Ina Salah zai koma idan ya bar Liverpool?

12 views

Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Masar, Mohamed Salah ya ce zai bar Liverpool a ƙarshen wannan kaka. To amma tambayar da masoya da masu bibiyar ƙwallon ƙafa ita ce ina zai koma da taka leda?

Salah, ya sanar da cewa zai bar Liverpool, bayan ya shafe shekaru tara a ƙungiyar tun bayan da ya koma kulob ɗin daga AS Roma a shekarar 2017.

Salah, mai shekaru 33, ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, inda ya ce lokaci ya yi da zai yi bankwana da kulob ɗin da ya bayyana a matsayin “gida”.

“Kun ba ni mafi kyawun lokaci a rayuwata. Wannan kulob ɗin zai ci gaba da zama gida a gare ni. Barin kulob ba abu ne mai sauƙi ba,” in ji shi.

Ita ma Liverpool ta tabbatar da cewa Salah zai bar ƙungiyar idan kwantiraginsa ya ƙare.

Salah shi ne ɗanwasan da ya fi samun kyaututtuka a tarihin gasar Fimiyar Ingila.

A tsawon shekarun da ya shafe a Anfield, Salah ya ci kwallaye 255 a wasanni 435, inda ya taimaka wa ƙungiyar lashe kofuna da dama ciki har da gasar Firimiya biyu da kofin Zakarun Nahiyar Turai.

Masana harkokin wasanni Alex Crook, Ben Jacobs da Fabrizio Romano duk sun ruwaito cewa kulob din ya amince Salah ya tafi ba tare da wani sharaɗi ba, duk da cewa a baya kwantiraginsa zai kai har shekarar 2027.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 4   +   4   =