Home SiyasaBa ƙabila ko addini ne ya kamata su ƙayyade shugaba ba — Peter Obi

Ba ƙabila ko addini ne ya kamata su ƙayyade shugaba ba — Peter Obi

10 views

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya ce zai amince da shan kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 idan aka gudanar da zaɓen cikin ’yanci, adalci da sahihanci.

Obi ya bayyana hakan ne a wata hira da aka watsa a gidan talabijin na Arise TV ranar Alhamis, inda ya ce zai mutunta zaɓin ’yan Najeriya idan suka zaɓi wani ɗan takara daban, domin hakan ne tsarin dimokuraɗiyya.

Sai dai tsohon gwamnan Anambra ya sake nanata cewa shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023, yana mai cewa waɗanda suka gudanar da zaɓen sun san abin da ya faru da kuma dalilin da ya sa aka samu matsala a tsarin zaɓen.

Game da batun rabon mulki bisa tsarin “turn-by-turn”, Obi ya ce bai kamata ƙabilanci ko addini su zama tushen zaɓen shugaban ƙasa ba. Ya ce yana da cancanta da ƙwarewar jagorantar Najeriya, tare da bayyana cewa ya yi karatu a manyan jami’o’i da cibiyoyin ilimi da suka haɗa da Oxford, Cambridge, Harvard, Columbia da Kellogg.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 2   +   9   =