- Hukumar Raba Arzikin Ƙasa ta Najeriya (RMAFC) ta sanar da cewa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na iya fara karɓar albashi tsakanin Naira miliyan 1.5 zuwa Naira miliyan 5 a duk wata, idan sabon tsarin ƙarin albashin masu riƙe da mukaman siyasa ya samu amincewar Majalisar Dokoki.
Hukumar ta bayyana cewa sabon tsarin ya shafi sake duba albashi da alawus-alawus na masu riƙe da manyan mukaman gwamnati, bisa la’akari da sauye-sauyen tattalin arziki da yanayin ƙasar.
A cewar RMAFC, shirin na buƙatar bin matakan da doka ta tanada kafin fara aiwatar da sabon tsarin albashin.
Sai dai, ƙarin albashin ba zai fara aiki kai tsaye ba, domin sai an samu amincewar Majalisar Dokoki ta Ƙasa kafin a aiwatar da sabon tsarin.

Albashin Tinubu na iya ƙaruwa kusan sau uku idan Majalisa ta amince.
17