Home LabaraiKotu Ta Umarci A Tura Ɗan Maina Gidan Yari Domin Fara Zaman Shekaru 7.

Kotu Ta Umarci A Tura Ɗan Maina Gidan Yari Domin Fara Zaman Shekaru 7.

34 views

 

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tura Faisal, ɗan tsohon shugaban rundunar yaƙi da almundahanar kuɗaɗen fansho, Abdulrasheed Maina, gidan gyaran hali domin ya fara zaman hukuncin ɗaurin shekaru bakwai da aka yanke masa.

Mai Shari’a James Omotosho ne ya bayar da umarnin, bayan Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ta shigar da buƙatar aiwatar da hukuncin da aka yanke wa Faisal a ranar 7 ga Oktoba, 2021.

An kama Faisal ne a ranar 14 ga Oktoba, 2026, bayan ya shafe kusan shekaru shida yana ɓuya sakamakon tsallake belinsa da kuma ƙin halartar shari’arsa.

Kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru uku a tuhume-tuhume na farko, shekaru bakwai a na biyu, da kuma shekaru uku a na uku, inda aka umarci hukuncin ya gudana a lokaci guda.

Alkalin ya kuma bayyana cewa za a fara ƙirga wa’adin zaman gidan yarin daga ranar 14 ga Oktoba, 2026, wato ranar da aka sake kama shi.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 1   +   9   =