Rundunar soji a Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa an kashe farar hula yayin hare-hare ta sama da aka kai a ƙauyen Tumfa da ke jihar Zamfara.
Kakakin rundunar, Micheal Onoja ya yi watsi da iƙirarin cewa an kai hare-haren ne kan farar hula.
Martanin nasa na zuwa ne bayan da ƙungiyar Amnesty da ke kare haƙƙin bil adama ta buƙaci gwamnati ta yi bincike kan rahoton zargin kisan farar hula fiye da 100 a wani hari ta sama da aka kai a kasuwar Tumfa da ke ƙaramar hukumar Zurmi.
Sai dai Manjo Onoja ya ce sojoji sun kai harin ne bayan samun bayanan sirri game da taron manyan jagororin ƴan ta’adda daga sassan yammacin Afirka.
Ya kuma ce a kan fararen hula aka shirya harin ba.
“Ba farar hula aka shirya kai wa hare-haren ba kuma ana yin komai domin kare su farar hular,” in ji shi.
Ya tabbatar cewa sojoji na gudanar da ayyuka a yankin inda ya ce suna ci gaba da yin aiki bisa tsarin dokar kare haƙƙin bil adama ta ƙasa da ƙasa.