Home SiyasaZaɓen Osun: APC Tayi Zargin An Shigo da ’Yan Daba Daga Legas.

Zaɓen Osun: APC Tayi Zargin An Shigo da ’Yan Daba Daga Legas.

13 views

Jam’iyyar APC a jihar Osun ta bayyana cewa tana zargin an shigo da wasu ’yan daba na siyasa cikin Gidan Gwamnatin Jihar Osun, ƙasa da sa’o’i 24 kafin gudanar da zaɓen gwamna na jihar.

 

Jam’iyyar ta ce hakan na iya yin barazana ga zaman lafiya da sahihancin zaɓen.

 

Da yake magana a madadin kwamitin yaɗa labaran kamfen na jam’iyyar, Mista Kehinde Ayantunji, a wani taron manema labarai a Osogbo, ya ce APC ta samu bayanan sirri cewa an shigo da dimbin ’yan daba daga jihar Legas zuwa Gidan Gwamnatin Osun.

 

Ya ce wasu da ake kira Olowe da Iberu ne ke jagorantar mutanen, waɗanda ake zargin an ba su masauki tare da goyon bayan Gwamna da tawagarsa.

 

Ayantunji ya yi zargin cewa an shigo da mutanen ne da nufin kawo cikas ga zaɓen, musamman a Osogbo da wasu sassan ƙaramar hukumar Egbedore, idan sakamakon zaɓen bai kasance cikin abin da jam’iyyar ke so ba. Ya ce bayanan sirrin jam’iyyar sun nuna cewa ana ganin mutanen suna shiga da fita daga Gidan Gwamnati.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 9   +   6   =