Gwamnatin Jihar Sokoto ta ce tana aiwatar da manyan ayyukan raya kasa ba tare da karbar bashi ba, inda ta fifita kashe kudade kan ayyukan ci gaba.
Kwamishinan Yada Labarai, Alhaji Sambo Bello Danchadi, ya bayyana cewa kasafin kudin 2026 ya ware kashi 70% domin ayyukan raya kasa, yayin da kashi 30% kawai aka ware don tafiyar da gwamnati.
Ya ce an kafa tsauraran matakan kula da kudi, ciki har da hana karin kudin kwangila da kuma biyan ‘yan kwangila kaso 30% tun farko domin hanzarta aiki.
Gwamnatin ta kuma aiwatar da ayyuka da dama, ciki har da gina tituna sama da 350, gyaran makarantu, fadada asibitoci da girka fitilun hasken rana.
Haka kuma, tana biyan bashin kudaden fansho da suka haura naira biliyan 14 ta hanyar tsarin biyan kudi a hankali.
A cewarsa, wannan tsari ya taimaka wajen gudanar da ayyuka cikin tsari da gaskiya, tare da kaucewa tara bashi da kuma tabbatar da dorewar ci gaba a jihar.